Banu umayya a kokarinsu na rufe hasken musulunci sun kirkiri tarin hadisai masu dimbin yawa domin soke darajar Ahlulbayt(a.s) ko kuma ba wadanda basu da daraja tarin darajoji. Dga cikin irin wadannan hadisai da suka kirkira, akawi hadisin nan wanda yayi suna a bakin malamai musamman a cikin watan Muharram wato hadisin Ashura wanda ake cewa manzon Allah yayi azumin Ashura kuma yayi umarni da ayi. Abdullahi bin Abbas ya fada cewa lokacin da manzon Allah[s.a.a.w] yazo madina ya riski yahudawa suna azumi a ranar 10 ga Muharram(Ashura) sai ya tambaye su dalilin daya sa suke azumi a ranar, suka ce masa saboda Allah ya kubutar da bani Isra'ila daga hannun fir'auna ne a irin ranar 10 ga Muharram shiya sa Annabi Musa ya azumci ranar suma suke yi. Sai Manzon Allah yace "ai mun fiku kusanci da Musa" daga nan sai ya azumci ranar ya kuma yi umarni da ayi. -Sahih Bukhari, mujalladi na 3, shafi na 222. -Mishkatul Masabih, bugun Delhi 1307BH, shafi na 172. (Abin lura: Mishkatul masabih yayi bayanin Manzon Allah(s.a.a.w) yayi azumi ne a ranar Ashura a shekara ta biyu bayan hijira, saboda a shekarar farko yazo madina ne a cikin watan Rabi'ul awwal) A wata fadar kuma, ibn Abbas ya fada cewa lokacin da Manzon Allah(s.a.a.w) yayi azumi a ranar Ashura kuma yayi umarni da ayi, sai sahabbansa suka ce dashi "ya ma'aikin Allah wannan rana, rana ce da yahudawa da nasara suka dauka da girma a wajensu" Manzon Allah ya amsa musu da cewar Insha Allah idan shekara ta zagayo zamu azumci ranar 9 ga wata. Amma sai manzo ya rasu kafin shekara ta zagayo. -Sahih Muslim 35, hadisi na 2528. Wani hadisin daya tafi hanya daban da inda wadannan suka nufa shine hadisin da Ummul Mumineena Aisha(r.a) ta ambata cewa kuraishawa sun kasance suna azumtar ranar 10 ga Muharram kafin bayyanar musulunci kuma Manzon Allah ma yana azumi a ranar, bayan yazo madina yaci gaba da azumin kuma yayi umarni da ayi. Lokacin da Allah madaukakin sarki ya wajabta azumin ramadan sai Manzo ya daina azumin Ashura, ya barshi a matsayin zabi in kaso kayi, in kaso ka daina. -Bukhari mujalladi na 3, littafi na 31, hadisi na 220. Mafi yawan yan'uwan mu Ahlussunna sun tafi akan duk hadisin daya zo a cikin Bukhari da Muslim sahihi ne, don haka ma suka rada musu suna sahihaini. Mu a wurin mu yan shi'a wannan ba haka yake ba saboda fadar Allah madaukakin sarki "shin basu kula da al-qurani kuma daya kasance daga wanin Allah, hakika da sun samu a cikinsa, saba wa juna mai yawa (Quran 4:82). Anan Allah Ta'ala na fada mana cewa duk wani littafi da ba hannunsa ya fito ba to tabbas akwai sabani a cikinsa mai yawa. Saboda wannan ne bama tsarkake littafanmu, kuma bamu yarda babu sabani a cikin kowane irin littafi muddin ba daga wurin Allah yake ba. To idan hakane bari mu diba wadannan hadisai mu gani sun inganta ko a'a. Allah Ta'ala yana cewa a cikin littafinsa mai tsarki "kada ku kasance kamar wadanda aka baiwa littafi gabanin haka, sai zamani yayi tsawo a kansu, saboda haka zukatansu suka kekashe, kuma mafi yawa daga cikinsu fasikai ne" (Quran 57:16). Abin lura anan shine Allah yayi muna umarni da kada mu kasance kamar (koyi da) yahudawa, saboda mafi yawansu fasikai ne (suna izgili ga Allah, sun canza ayoyinsa, sannan sun butulce masa bayan ya wadata su da ni'imar sa). Sannan Manzon Allah ya umarcemu da kada mubar gemu irin yanda mutanen littafi suke bari. Lalle ko Manzon Allah bazai taba koyi da yahudawa ba ta kowace irin siga kuwa. Wani karin abin lura shine yanda hadisan suke sabani da junansu ta yanda har akwai hadisin da aka ce yahudawa walima suke yi a ranar sai Manzon Allah yace ayi azumi don a saba musu. -Sahih Bukhari hadisi na 1866. Karin hujjar rashin ingancin wadannan hadisai itace Jabir bin Abdullah ya ambata cewa Umar bin Khattab yazo da Attaurah gaban Manzon Allah yace "wannan itace Attaurah" amma Manzo bai amsa masa ba, sai shi Umar ya fara Karanta Attaurah din. Take fuskar Manzon Allah ta canza, sai Abubakar yace shin baka ga fuskar ma'aikin Allah bane? Daga nan Umar yace "ina rokon afuwa gareka ya Allah daga fushin ka da fushin Annabinka, lalle ne mu munyi imani da ubangijinmu shine Allah, musulunci a matsayin addini, da Muhammad a matsayin Manzon Allah." sai Manzon Allah yace masa "na rantse da wanda rayuwar Muhammad take a wurinsa da Musa zai bayyana a gabanka kuma ka bishi ka kyaleni, to da tabbas ka tabe; domin koda Musa na raye(yanzu) ya riske ni a matsayin Manzon Allah to babu shakka zai bini. -Tirmidhi, hadisi na 194. Tambaya anan itace shin Manzon Allah ne yabi Annabi Musa ko Annabi Musa ne yabi Manzon Allah bisa ga abunda wadancan hadisai suka nuna? A hakikanin gaskiya yahudawa sun kasance suna da watanninsu. To ya aka yi suke yin azumi 10 ga Muharram? A zamanin da ne, gidaje biyu na 'yayan Ibrahim(a.s) suke kara wata bakwai a cikin kowace shekara goma sha tara (intercalating) saboda watannin kalanda suyi daidai da kwanaki 365 na zagayawar duniya (irin misalin abunda bature ke kara kwana daya a fabrairu bayan kowane karni guda) saboda wannan ne ma watan yahudawa na bakwai wato TISHRI 1 yayi daidai da watan Muharram na shekarar musulunci, wato goma ga Tishri 1 na daidai da goma ga Muharram. Kuma tabbas ba ranar ne yahudawa suke azumi ba saboda fadar littafin su cewa cikin watan ABIB ne Allah Ubangijinku ya kubutar da ku a Misra cikin dare (Deut, 16:1). Watan Abib kuma yana daidai da watan Rajab ne a cikin shekarar Musulunci. Theodore H. Robinson da W.O.E Oesterley sun ambata cewar Rajab (Sic) yana daidai da watan Abib na Hebrew. -Hebrew religion S.P.C.K bugun London a 1955 shafi na 128. Duk da cewa bayan shekara tara da yin hijira Manzon Allah ya hana kara kwanaki ko watanni a cikin shekara (wato aka hana intercalating) amma bincike ya tabbatar da cewa lissafin ya dade da bata a hannun larabawa, don haka ne ma Muharram na shekara ta biyu bayan hijira ya fara a ranar 5 ga July shekara 623 bayan haihuwar Annabi Isah (as), watanni da yawa kafin Tishri 1 ( wanda ko d yaushe yake daidai da September ko October), wanda da tabbas yahudawa suna azumi a ranar 10 ga Tishri 1 ne, to ba zai kama Muharram ba sai dai September ko October wadanda suka yi daidai da Rabiul Awwal na waccan shekarar ta biyu bayan hijira. To tunda bayani ya tabbata karara a littafin su cewa suna azumi ne a cikin watan Abib shima bincike ya nuna zai y daidai da March ko April wadanda suka yi daidai da Rajab ko Sha'aban na waccan shekarar ta biyu bayan hijira. Hakika shi dai wanda ya kirkiri wadannan hadisai ya yi la'akari ne kawai da cewa Muharram na daidai da watan 7 a wajan yahudawa ba tare da sanin cewa shin suna azumi 10 ga watan 7 din ko ba sa yi. Wadannan hadisan da ma wasu tarin hadisan misalin a ranar 10 ga Muharram ne Allah ya saukar da jirgin Annabi Nuhu (as) bisa turba, a ranar ne wuta tayi sanyi ga Annabi Ibrahim (as), a ranar ne Allah dauke Annabi Isah zuwa sama, duka kirkirar banu Umayya ne domin su rufe gaskiyar abunda ya faru a ranar Ashura (10 ga Muharram) na kashe dan Manzon Allah (sawa) a filin dajin hamadar Karbala. Alhamdu lillahi mun gode wa Allah da ya sada mu da jagoran gaskiya wanda ya bayyana muna hakikanin abunda ya faru a ranar Ashura wato Sayyid Ibrahim Yakub Zakzaky (H), da fatar Allah ya kara masa kariya, kwarjini, haiba da kamala ya kuma kara fadada kirjin sa don y ci gaba da bayyana mana makidojin banu Umayya muna ganin wallensu, albarkacin Imam Mahdi ( AF). Ahmad Salisu da Hisham Salisu Aliyu Gusau (ahmadsalisualiyu@gmail.com) (hishamsalisu@ymail.com) |
AHMAD SALISU ALIYU
Thursday, 12 January 2012
Azumin Ashura
Subscribe to:
Posts (Atom)
